1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coranavirus ta haddasa dakatar da wasanni

Abdourahamane Hassane
March 18, 2020

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA ta ɗage gasar cin kofin nahiyar Turai na kwallon kafa wanda ya kamata a yi a cikin watan Yuni na wannan shekara har zuwa shekara ta 2021 saboda annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3ZcJr
Coronavirus UEFA Absage Spiele der Champions League und Europa League
Hoto: picture-alliance/empics/M. Egerton

A da an shirya yin gasar a cikin watan Yuni na wannan shekara har zuwa 12 ga watan Yuli, sai dai annobar Coronavirus ta janyo dakatar da wasan. Wannan shi ne karo na farko cikin shekaru 60 a aka ɗage gasar ta neman zakara na wasannin kwallon kafar na nahiyar Turai.