1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wane mataki shugaba Buhari zai dauka bayan dawowarsa?

Ramatu Garba Baba ATB
August 19, 2017

Tun bayan saukar shugaban Najeriya Muhammad Buhari Abuja babban birnin kasar bayan jinyar tsawon lokaci a Birtaniya, al'ummar kasar ke gudanar da bukukuwar nuna farin cikinsu.

https://p.dw.com/p/2iVs7
Nigeria Muhammadu Buhari in London
Hoto: Reuters/Nigeria Presidency

 

A Mahaifar Shugaba Buharin watau jihar Katsina tun cikin daren Asabar ake kade-kade da raye-raye
wasu mutanen na kalamai dabam-dabam na maida martini da kakkausan afazi ga masu kira ga Shugaban kasar ya yi murabus.

A safiyar Lahadi ma kuma an tashi da wasu kade-kaden na murna da ya hada kungiyoyin farar hula wadanda suka yi dafifi a gaban gidan gwamnatin Katsina inda suka mika wa gwamna Aminu Bello Masari takarda da zai gabatarwa Shugaba Muhammadu Buharin ta nuna goyon baya a gare shi da gwamnatinsa.

A jawabin da ya yi bayan karbar kungiyoyin gwamna Masari ya bayyana cewar ba bu wani ma'auni da za su iya amfani da shi na kwatanta farin cikin su da komowar shugaban kasar.

Mutane da dama a wajen wannan gangami sun rinka kalamai da kakkausan lafazi suna maida martini ga masu kira ga Shugaba Buharin ya yi murabus. Malam Sabo Musa na kungiyar Network for Justice ya ce komawar Buharin ta gama da duk wasu mutanen da ke surkulle don kada ya koma kasar.

Daruruwan mutane ne da suka hada Maza da Mata daga kungiyoyi dabam-dabam suka hada wannan gangamin, Hajiya Rabi Muhammad  ta Coalition for Civil Societies ta bayyana cewar mutanen da ke kira ga Shugaba
Buhari ba su tsoron Allah ne sai Buhari saboda almundahana da suke tafkawa, shi yasa suke neman ya sauka ko ma Allah ya dauki ransa.

Abinda mutane suka zura ido su gani a yanzu shi ne kuma matakan da Shugaba Buharin zai dauka na farfado da harkar tsaro da tattalin arziki manyan abubuwan da ya yi alkawarin zai gyara, wadanda a yanzu suka tabarbare.