Wasanni: 13.01.2025
January 13, 2025Bayan dawowa daga hutun hunturu da kungiyoyin da ke bugawa a gasar lig din Jamus wato Bundesliga suka yi, ga dukkan alamu Borussia Dortmund ba ta dawo wannan hutu da kafar dama ba.
A wasanta na farko a mako na 16 da ta fafata da makwabciyarta Bayer Leverkusen da ke rike da kambu, ta karya kofin Dortmun din.
Yadda ba ta taba gaza yin nasara a duka wasannin da ta buga a gida a wannan kaka ba ta hanyar bin ta har gida ta kuma lallasata da ci uku da biyu a wasan yaye kallabin dawowa hutun hunturu da suka buga a ranar Jumma'ar da ta gabata.
Wannan rashin nasara dai, ya sanya Dortmund din ci gaba da zama a matsayi na bakwai a teburin kakar Bundesliga ta bana.
A sauran wasannin da aka fafata a Asabar din karshen mako kuwa, Mainz ta samu nasara a gida a wasanta da Bochum da ci biyu da nema.
Kamar yadda Heidenheim ta karbi bakuncin Unioin Berlin ta lallasata da ci biyu da nema kana Freiburg ma a gidan ne ta samu nasara a wasanta da Holstein KIel da ci uku da biyu.
Ita kuwa Frankfurt ta bi St. Pauli ne har gida ta kuma lallasa ta da ci daya da nema, kamar yadda Wolfsburg ma ta bi Hoffenheim har gida ta caskara ta da ci daya mai ban haushi.
To yayin da aka dawo hutun hunturun na kakar Bundesliga ta Jamus, wakilinmu na Kaduna a Najeriya Muhammad Muhammad ya jiyo mana ra'ayin magoya baya kan yadda suke fatan kakar da bana ta karkare.
A gasar Cin Kofin Kalubale na Ingila kuwa da aka fafata a karshen mako, kungiyoyi dabam-dabam sun taka rawar gani wasu kuma sun sha kashi.
Wasan da ya fi daukar hankali shi ne karawar Tottenham da 'yar karamar kungiya Tamworth, inda Tottenham din ta tsallake rijiya da baya.
Da kyar da jibin goshi ne dai bayan an tashi daga wasan canjaras babu ci, Tottenham din ta samu nasara da ci uku da ne kafin a kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Tun da fari dai, a mintuna na 101 ne dan wasan Tamworth mai masaukin baki ya ci gida, inda a mintuna na 107 dan wasan Tottenham din ya kara kwallo ta biyu kafin su zura ta uku a mintuna 118 ana daf da tafiya bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Ita kuwa Arsenal wasan bai mata dadi ba, domin bayan kwashe mintuna 120 suna fafatawa da bakuwarta Manchester United kunnen doki daya da daya, United din ta lallasa mai masaukin bakin nata da ci biyar da uku a bugun daga kai sai mai tsaron gida.