Inda aka kwana a gasar cin kofin Turai
June 14, 2021Za mu dauko shirin da wasannin neman cin kofin kwallon kafa na kasashen Turai da aka fara, wanda tun farko aka jinkirta daga shekarar da ta gabata saboda bullar annobar cutar coronavirus da duniya ta fuskanta. A wasan da aka kara a wannan Lahadi, inda Ingila ta samu galaba kan Kuroshiya da ci daya da nema, kana Ostiriya ta doke Mocedoniya ta Arewa da ci uku da daya, yayin da Holland ta doke Ukraine da ci uku da biyu.
A Brazil an fara wasan neman cin kofin kasashen Latin Amirka, duk da cewa kasar tana cikin kasashen duniya da suka fi samun matsalar annobar cutar coronavirus, inda mai masaukin baki Brazil ta doke Venezuela da ci uku da nema. A wasan lokacin bazara na mata na kwallon kafa na kasa da kasa kuwa, Najeriya ta tashi uku da uku a wasa da kasar Potugal a karshen wannan makon. Wasan da ke gudana a Amirka, tun farko Amirka ta samu galaba kan Potugal da ci daya mai ban haushi. A wasan Tennis na French Open da aka kammala wanda ake yi wa lakani da Roland Garros, shaharren dan wasa Novak Djokovic dan kasar Sabiya ya lashe rukunin maza bayan doke Stefanos Tsitsipas dan kasar Girka.