1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Lyon ta lashe kofin zakarun Turai na mata

Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
August 31, 2020

Robert Lewandowski ya zama dan kwallon shekara a Jamus. Ina makomar Lionel Messi? Matan Lyon sun lashe gasar Champions League na mata.

https://p.dw.com/p/3hoxG
Frauen UEFA Champions League | Finale - VfL Wolfsburg vs Olympique Lyonnais | Torjubel (0:1)
Hoto: Reuters/G. Bouys

Dan wasan kwallon kafa na kungiyar Bayern Munich Robert Lewandowski ya lashe kambun dan wasan kwallon kafa na shekara na Jamus. Lewandowski mai shekaru 32 a duniya wanda ya fi kowa zura kwallo a raga a kakar wasannin Bundesligar Jamus ta bana, ya lashe gasar ne bayan da mafi aksarin 'yan jaridu marubuta labarin wasanni a Jamus din suka zabe shi, kamar yadda mujallar wasanni ta Kicker ta ruwaito. Haka kuma mai horas da 'yan wasan na Bayern Munich Hansi Flick ya lashe kambun mai horas da 'yan wasa na shekara a Jamus din. Wannan nasara dai ta biyo bayan lashe kambun wasanni uku da kungiyar kwallon kafar ta Bayern ta Jamus ta yi a wannan shekarar, inda ta lashe kofin lig-lig na Jamus wato Bundesliga ta kuma lashe kofin kalubale na Jamus din da kuma kofin zakarun nahiyar Turai. Lewandowski dan asalin kasar Poland, ya bayyana cewa ya yi matukar alfahari da lashe wannan kambu da ya yi, inda ya ce a kowacce shekara yana da wannan fata, sai dai kuma gaza kai wa ga lashe kambun bai taba sanya shi ya yi kasa a gwiwa ba, har sai da ya cimma burinsa.

Robert Lewandowski ya lashe kambun dan wasan kwallon kafa na shekara na Jamus
Robert Lewandowski ya lashe kambun dan wasan kwallon kafa na shekara na JamusHoto: picture-alliance/SvenSimon/F. Hoermann

Lewandowski dai ya samu galaba da kuri'u 276 yayin da Thomas Müller shi ma daga Bayern din ya samu 54 shi ma Joshua Kimmich na Bayern da ya zo na uku ya samu kuri'u 49. Lewandowski  ya jefa kwallaye 34 a kakar Bundesliga ta bana, yayin da ya jefa kwallaye 15 a gasar zakarun Turai wato Champions League ya kuma jefa kwallaye shida a gasar kofin kalubale na Jamus.

A hannu guda kuma 'yar wasan kungiyar kwallon kafa ta VfL Wolfsburg Pernille Harder ta samu nasarar lashe kambun 'yar wasan shekara ta Jamus din. Mai shekaru 27 ta lashe kambun 'yar wasan kwallon kafa ta shekara da kuri'u 212 daga cikin 446 da aka kada, inda Alexandra Popp ita ma daga kungiyar ta Wolfsburg ta samu kuri'u 76 kana Dzsenifer Marozsan ta kungiyar Olympic Lyon da ta lashe kambun a shekarun 2017 da 2018 da kuma 2019 ta zo ta uku da kuri'u 36.

Lyon ta Faransa ta lashe kofin zakarun Turai bangaren mata

Mako guda bayan kammala gasar zakarun Turai bangaren maza, su ma mata sun gudanar da nasu wasan karshe a ranar Lahadi tsakanin Olympic Lyon ta Faransa da takwarorinsu na Wolfsburg. Sai dai sabanin maza inda kungiyar Bayern Munich ta Jamus ta doke PSG ta Faransa, akasin haka aka samu a rukunin mata, inda Lyon ta samu nasarar lashe gasar zakarun Turai bangaren mata, bayan da ta lallasa takwararta ta Wolfsburg da ci uku da daya.

Kwallon kafar mata na kara samun karbuwa a Turai
Kwallon kafar mata na kara samun karbuwa a TuraiHoto: Getty Images/AFP/V. Lopez

Tun dai kafin a tafi hutun rabin lokaci ne, Lyon din ta yi nasarar zura kwallo biyu a ragar Wolfsburg din, inda bayan da aka dawo hutun rabin lokaci ta kara kwallo daya a ragar Wolfsburg din yayin da su kuma suka yi nasarar zura kwallo daya a raga, a wasan karshe da suka buga a ranar Lahadi a kasar Spain.

Makomar Lionel Messi a Barcelona

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta kasar Spain, ta bayyana cewa har yanzu shahararren dan wasanta, Lionel Messi na karkashin kwantiraginta, sa'o'i kalilan bayan Messi ya gaza halartar gwajin gabanin fara kakar wasanni da ake wa 'yan wasan kungiyar. Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kasar Ingila dai ta nuna sha'awarta da kuma fata na sayen dan wasan dan asalin kasar Ajantina. Sai dai hukumar kula da wasannin lig-lig din Spain din ta La Liga, ta sanar da cewa ba za ta amince Messin ya tafi wata kungiyar ba har sai ya biya zunzurutun kudi Euro miliyan 700 kamar yadda yake cikin sharuddan kwantiraginsa. A ranar Talatar da ta gabata ne dai Messi ya bayyana cewa zai bar kungiyar, a kokarinsa na yin amfani da wata sadara cikin kwantiragin da ya sanyawa hannu a shekara ta 2017, da ta ba shi damar komawa wata kungiyar a kowanne karshen kakar wasanni.

Ko zo a samu fahimtar juna tsakanin Messi da Barcelona?
Ko zo a samu fahimtar juna tsakanin Messi da Barcelona?Hoto: picture-alliance/Sven Simon/F. Hörmann

Sai dai Barcelona, ta ba shi amsa nan take, inda ta ce wa'adin wannan sadarar ya jima da karewa, a dangane da haka ba zai iya tafiya salim-alim ba, tilas ya biya wadannan zunzurutun kudade. Ana dai rade-radin Messin zai koma kasar Amirka, yayin da bayan Manchester City, kungiyar kwallon kafa ta PSG ta kasa Faransa ma ta shiga jerin kungiyoyin kwallon kafar da ake hasashen zai koma.

Hamilton na ci gaba da mamaye tseren motoci na Formula 1

Shararraen dan tseren motocin nan da ke tuka mota kirar kamfanin Mercedes Lewis Hamilton ya samu nasara a karo na biyar cikin tsere bakwai da suka yi a baya-bayan nan, abin da ke kara nuni da nasarar da yake kara tunkarta a kakar ta bana a kan abokin tseren nasa da ke mara masa baya Max Verstappen. A yanzu Hamilton na da maki 157 a kakar tseren motocin na Formula 1 a bana.