Za a dama da Super Eagles a gasar AFCON ta 2022
March 29, 2021Hasali ma Super Eagles ta cancanci shiga gasar tun ma kafin ta buga da Benin bayan da Lesotho da Saliyo suka tashi wasansu ba wanda ya ci wani, lamarin da ya faranta ran magoya bayanta saboda dama Najeriya ta kasance giwa a fannin kwallon kafa a Afirka, duk da tarin matsalolin da suka dabaibaye babbar kungiyar kwallon kafarta da hukumumar kwallon kafarta. Tuni ma ma'abota kwallon Najeriya suka fara tafka muhawara kan rawar da Super Eagles za ta iya takawa a gasar Afirka ta 2022.
A ranar Lahadi dai aka fara yini na shida kuma na karshe na wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Afirka ta badi. A karawa da ta yi da Afirka ta Kudu, Sudan ta bai wa marada kunya inda ta lallasa Bafana Bafana da 2-0, lamarin da ya ba ta damar samun daya daga cikin tikiti bakwai da suka rage na zuwa kasar Kamaru a 2022. Kwallayen da Saifeldin Malik da Mohammed Abdelrahman suka zura ne suka bai wa Sudan damar cika maki 12 da suka bude musu kofar gasar AFCON a karo na tara cikin trhitin kasar.
Ita ma Ghana da ke rukuni na uku ta lallasa tsibirin Sao Tome da Principe da 3-1 ba tare da wata wahala ba. Sai dai wasan ya kasance na ran Sarki ya dade ga "Black Stars" saboda ta riga ta kai banteta tun wasannin bayan.
A sauran wasannin kuwa, a rukunin A, Namibiya ta doke Guinea Conokry da 2-1 ba tare da nasarar ta kawo mata ci gaba ba saboda ta riga ta cancanci shiga gasar kwallon kafa ta Afirka. Mali ce ta kasance kasa ta biyu da ta haye sakamakon dakatar da kasar Chadi daga dukkanin al'amuran wasanni da CAF ta yi saboda katsalandan da hukumomin Ndjamena ke yi wa kwallon kafa. Ita kuwa Tunisiya ta doke Equatorial Guinea da 2-1, lamarin da ya sa ta zama daya-dayar kasa da ta kammala wasannin share fage ba tare da baras da ko da wasa daya ba. A wannan rukuni na 10 dai Tanzania ta sami nasara a kan Libiya (1-0) a birnin Dar-es-Salaam.
Daga cikin kasashen da suka samun tikitin gasar da za ta gudana daga 15 ga Janairu zuwa Fabrairu 28 2022, har da Kamaru wacce ke karbar bakuncin gasar, da Aljeriya da ke da kofin, Senegal, Tunisia, Mali, Burkina Faso, Guinea, Comoros, Gambiya, Ghana, Gabon, Equatorial Guinea, Zimbabwe, Morocco, Cote d' Ivoire, Masar, Sudan, da Najeriya.
A nahiyar Turai kuwa, kasashen sun kara da juna da nufin share fagen shiga gasar kofin duniya ta 2022, inda kwanaki kalilan bayan da Jamus ta lallasa Island da ci uku da nema, a karshen mako Jamus din ta doke Rumaniya da ci daya mai ban haushi. Serge Ngnabry ya zura daya dayan kwallon a minta 16 da fara wasa. Jamus za ta yi wasanta na gaba a ranar Laraba da Mecedoniya, kuma Jamus tana kan gaba a wannan rukuni da maki 6.
A sauran wasanni kuwa Faransa da ke rike da kofin duniya na kwallon kafa ta sami nasara a kan Kazakstan da 2-0, alhali ta tashi ci daya ko ta'ina da Ukraine a wasanta na ranar Laraba.
A rukuni na biyu, Spain ta farfado bayan canjaras da ta yi da Girka, inda ta lallasa Jorjiya da 2-1, kuma ta kasance a sahu na biyu a rukuninta, yayin da Sweden ta yi kaca-kaca da Kosovo 3-0.
A rukuni na uku, Italiya kamar a wasan farko ta yi nasara a wasanta na ranar Lahadi inda ta gasa wa Bulgeriya aya a hannu da ci 2-0. Italiya na kankanka a yawan maki da Switzerland wacce ita ma ta samu nasara a dukkanin wasanninta.