WHO ta damu da karuwar corona a Turai
August 30, 2021Talla
A makon da ya gabata an sami karuwar kashi 11 cikin dari na mace-mace a yankin inda wasu alkaluma ke cewa ana tsammanin za a sami mutum 236, 000 da za su rasu zuwa daya ga watan Disambar wannan shekarar a cewar darakta mai kula da nahiyar turai a hukumar lafiyar ta duniya Hans Kluge kamar yadda ya shaidawa manema labarai a Copenhagen.
Kawo yanzu mutum miliyan daya da dubu dari uku suka rasu a sakamakon cutar Corona a nahiyar Turai tun bayan barkewar annobar.