Yaɗuwar ɓarɓashin nukiliya a Japan
March 27, 2011Talla
Mahukunta a ƙasar Japan sun ɗauke ma'aikata dake aiki a tashar nukiliya ta Fukushima, bayan da suka gano tarin sinadarin nukiliya wanda ya tsiyayo daga tukunyar sarrafa dagwalon makamashin nukiliya ta biyu. Kamfanin samar da lantarki na birnin Tokyo ya sanar da cewa yawan sinadarin da aka gano a tashar ta nukiliya ya rumɓinya har sau miliyan goma bisa ƙa'iada, abinda ke nuni da cewa tukwanen sun samu mummunan lahani.
Ɓarɓashin nukiliyan da aka gano a cikin teku da ke kusa da tashar nukiliyan, shima ya haura mizani har sau 1,800. Alƙaluman hukama kan yawan waɗanda suka mutu sakamakon gigizar ƙasar ta Japan, yanzu ya kusan 10,500 yayin da wasu mutane kimanin 10,700 suka ɓace.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Yahouza Sadissou Madobi