1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yadda wakilan duniya ke kallon zaben Mali

Ahmed Salisu
July 31, 2018

Al'ummar Mali na dakon sakamakon zaben shugaban kasa da masu sanya idanu suka yaba da shi. Ko da yake akwai 'yan kura-kurai nan da can da aka samu.

https://p.dw.com/p/32Nvx
Mali Wahlen
Hoto: Imago/Le Pictorium/N. Remene

A cikin sharhin da ta rubuta, Katrin Gäinsler ma'aikaciya a tashar Dw, ta ce wakilan kungiyar Tarayyar Turai da suka sanya idanu kan zaben sun yaba da yadda ya gudana kasancewar ba a fuskanci tashin hankali na a zo a gani ba a rumfunan zabe sai dai a share guda an fuskanci matsala ta satar akwatunan zabe a wasu yankuna na arewacin kasar, kana a wasu sassan kasar an samu rahotanni na tursasa wa jama'a su zabi abin da ba su yi niyya ba; sannan abin tambaya shi ne dukannin rumfunan zaben kasar dubu 23 ne suka bude lokacin zaben? Ko ma dai ya lamarin yake, ba a yi zaton za a kwashe lafiya a lokacin zaben ba kasancewar a 'yan shekarun nan kasar ta fuskanci matsaloli iri-iri musamman ma na tsaro.

Mali - Französische und malische Truppen töten in Mali 30 Dschihadisten
Hoto: Getty Images/AFP/D. Benoit

Mali dai na kan gaba a kasashen da dakarun kasashen Turai ke girke inda suke aikin wanzar da zaman lafiya. Faransa na da dakaru dubu 4 da 500 yayin da Jamus ke da sojojinta kimanin 700 sai kuma dakarun MINUSCA da yawansu ya haura dubu 13.

 

Aikin da wadannan dakarun ke yi, ya taimaka wajen samar da zaman lafiya a arewacin kasar, sai dai da zarar an samu ban iska sai ka ga karin hare-hare sun sake dagula lamura. Faruwar hakan kuwa ba za ta rasa nasaba da irin yadda al'umma ke kin tallafa wa dakarun na MINUSCA ba. To sai dai wani abin yabawa shi ne irin tallafin da suka bada wajen kai kayan zaben a sassan kasar dabam-dabam wanda ba don haka ba da aikin da ke da wuyar gaske ba zai yiwu ba.

Wata matsala har wa yau da kasar ke fuskanta, ita ce irin yadda dakarun gwamnati ke cin zarafin al'umma inda wasu lokutan suka bude wuta irin na kan mai tsautsayi kamar yadda hukumar nan da ke kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta nunar, ko da dai wani horo da aka bijiro da shi don wayar musu da kai kan mutunta hakkin dan Adam ya taimaka wajen ilimantar da kashi 60 cikin 100 na sojin kasar.

Mali UN-Mission MINUSMA | Kampfhubschrauber Tiger
Hoto: picture-alliance/dpa/Bundeswehr/M. Tessensohn

Duk da wannan, har yanzu tsakiyar kasar na cikin tsaka mai wuya saboda matsala ta tsaro, haka ma abin ya ke a kudanci. Tashin hankalin da ake fuskanta na da nasaba da rikici irin na kabilanci don ko a makon da ya gabata ma sai da aka hallaka mutanen da yawansu ya kai 17. Irin wannan matsala ta saba da wadda ake gani a arewaci inda galibin hare-haren da akan kai suke karewa kan dakarun kasashen waje ko da dai a karshe talakawa na samun nasu kason. Da dama na ganin cewar an yi watsi da irin wadannan matsaloli da ya kamata a ce an magance tun tuni.

Al'umma da dama a Mali sun daina amincewa gwamnati hakan kuma ya sanya wasu sun yi shakulatin bangaro da wannan zabe da aka yi. Irin muhimmanci da ake jingina wa bada horo ga dakarun kasar ya kamata a ce an jingina kan yakar ta'addanci da kuma fadace-fadace tsakanin kabilu. Kyautuwa ya yi a ce hukumomi sun matsa kaimi wajen tabbatar da tsaro domin sai da tsaro ne ake samun cigaba mai ma'ana. Baya ga tsaro ma dai akwai bukatar yin aiyyukan raya kasa kamar samar da makarantu da asibitoci kasancewar da dama sun lalace sannan a samawa mutane aikin yi da kuma sana'o'i.

Mali Douentza Markt Frauen Lebensmittel
Hoto: AFP/GettyImages

Kalubalen da ke gaban sabuwar gwamnatin da za a kafa a Mali na da yawa amma abu da ya kamata a ce ta maida hankali a kai shi ne tantace matsalar tsaro da maganceta cikin gaggawa kuma ya kamata a ce an dama da al'ummar kasar wajen kawar da wannan matsala. Yin hakan ne kawai zai sanya al'umma su kasance suna goyon bayanta sannan ta haka ne za a samu zaman lafiya mai dorewa.