1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS: An fito da tsari muhimmi a taron birnin Ouagadougou

Salissou Boukari AAI
September 16, 2019

Kungiyar kula da tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ta CEDEAO ko ECOWAS ta fitar da sabon tsari domin fuskantar barazanar ta’addanci da tsattsaurar ra’ayi a cikin ‘yan shekaru masu zuwa.

https://p.dw.com/p/3Pgyt
Taron ECOWAS a birnin Ouagadougou
Taron ECOWAS a birnin OuagadougouHoto: DW/Katrin Gänsler

Wannan tsari mai girman gaske da kungiyar ta kasashen Yammacin Afirka ta shinfida domin yaki da matsalar tsaro a tsakanin kasashe zai soma ne daga shekara mai zuwa ta 2020 zuwa shekara ta 2024, ko ma da yake sai a babban zaman taron kungiyar da za a yi na watan Disamba mai zuwa a birnin Abuja na tarayyar Najeriya ne za a tabbatar da tsarin, inda kasashe mambobi suka sha alwashin tattara kudaden da yawansu ya kai miliyan dubu daya na dallar Amirka. Wanda a cewar shugaban kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO kuma shugaban jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou, tattara wadannan kudade shi ne zai tabbatar da aniyarsu ta neman cima wannan buri.

 

Sai dai a cewar Maman Sani Adamou wani dan fafutikar ci gaban kasashen Afirka:

''Kudaden dai da kungiyar ta ECOWAS ta sha alwashin tattarawa, za a hadasu ne a cikin shekaru biyar daga shekara mai zuwa ta 2020, kuma shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar ta ECOWAS Jean Claude Brou shi ne zai sa ido kan yadda ko wace kasa mamba za ta bada nata kason wanda ake rade-radin cewa kungiyar UEMOA ta masu kudin bai daya na yammacin Afirka za ta bayar da rabin kupadan da ake bukata sannan daga bisani a yi tsari kan yadda ko wace kasa za ta bayar da nata kaso na sauran kudaden da suka rage kuma cikin kasashen har da Chadi da Mauritaniya da ba sa cikin kungiyar ta ECOWAS amma kuma suna cikin kungiyar G5 Sahel''. 

Karte Infografik ECOWAS WAMZ ENG

Sani Roufa'i Malami ne a jami’ar birnin Damagaram kuma manazarci kan al’amuran yau da kullum:
''Manyan ayyukan da za a yi dai da waddan kudade shine na bayar da horo ga jami’an yaki da ta’addanci, da sauran manyan laifuka, kaman irinsu safarar makammai, da muyagun kwayoyi, da Taba da dai sauransu wanda ake ganin masu wannan aiki na daga cikin masu assana rashin zaman lafiya a tsakanin kasashen.

Sai dai a cewar Maman Sani Adamou maganin wadan nan matsaloli su ne mulki na adalci:

''A mataki na karshe dai wannan gidauniya ta kasashen na ECOWAS za ta bada damar samar da wata cibiyar tattara bayannan sirri da za ta amfanni dukannin kasashen domin dakile duk wata muguwar aniya ta masu aikata laifuka da sauran manyan ‘yan ta’adda''.