'Yan adawa sun kaurace wa tagwayen zabukan Chadi
December 29, 2024Rabon Chadi ta shirya Zaben 'yan majalisar dokoki tun shekara ta 2011, kuma dalilai da suka kai ta ga jinkirta wannan muhimmi mataki na tsarin dimukuradiiya sun hada da barazanar hare-haren ta'addanci da matsalolin kudi da annobar coronavirus da kuma uwa uba sauyin da ya biyo bayan mutuwar Shugaba Idris Deby. Maimakon haka ma, gwamnatin mulkin soja ta nada majalisar rikon kwarya da ta kunshi mambobi 93.
Karin bayani: Chadi: Cin hanci da karbar rashawa na karuwa a mulkin Deby
Christian Baïdessou, masani kan harkokin zabe na kasa da kasa, ya nuna takaici game da rashin samun kwararar masu kada kuri'a inda ya ce: "Mun yi tsammanin cewar mutane za su fi haka, amma abin takaici, hakan bai faru ba. Baya ga wasu 'yan rangadin da ya shafi manyan jami'an gwamnati, da suka yi amfani da kudin kasa kamar yadda aka saba, galibin matasan 'yan takarar da na zanta da su suka ce son yin kamfen na gida-gida, wanda ya yi daidai da karfinsu."
Sai dai 'yan adawa na Chadi sun yin tir da abin da suka kira salon mulkin kama karya da danniya da gwamnatin farar hula da a zaba a watan Mayun 2024 ta runguma, lamarin da ya sa madugun adawa Succès Masra ya kaura ce ma zaben. Hasali ma dai, shugaban jam'iyyar Reformateur ya dora wa gwamnatin Deby alhakin zubar jini yayin zanga-zangar adawa da kuma kisan gillar da 'yan sanda suka yi a ranar 9 ga Mayu, 2024.
Karin bayani: Chadi: Kotu ta tabbatar da nasarar Deby
Kakakin 'yan adawa Max Kemkoye ya bayyana cewar kura-kuran da ke cikin dokar zabe ne ya hana su shiga a dama da su, inda ya ce: "Muna kin amincewa da tsarin zaben da ba a bi ka'ida wajen kafa shi ba. Misali, hukumar zabe ta kasa (ANGE) tana kin mika rahoto da ke dauke da sa hannu wakilai na runfunar zabe, kuma tana kin wallafa sakamakon a rumfunan zabe da kuma kin bayyana sakamakon zabe a mazabu. Baya ga haka, cikakken ikon da gwamnati ke da shi a kan hukumar zabe da kotun tarin mulki, ya sa wannan tsari na zabe ba shi da inganci."
Shugaban kasar Chadi Mahamat Deby Itno ya ci gaba da amfani da kafofin sada zumunta wajen nuna muhimmancin zabukan, wanda ya ce za su ceto kasar daga tarkon fadawa cikin rudani tare da samar da ci-gaba mai dorewa. Saboda haka ne ya nemi wadanda suka yi rejista da su sauke nauyin da ya rataya musu a wuya a matsayin 'yan kasa.
Shi ma François Djekombé, shugaban jam'iyyar USPR kuma dan takarar zaben 'yan majalisar dokoki, ya ce bai ga fa'idar kaurace wa wadannan zabukan ba. Ya ce: "' Ko mun shiga wadannan zabuka ko ba mu shiga ba, harkokin kasarmu za su ci gaba da tafiya. Ina tsammanin maimakon ka ce: "Idan na yi zabe, me zai canza? ", kamata ya yi mu tambayi kanmu: "Shin kin kada kuri'a zai canza wani abu?"
Karin bayani: Kulla alakar tsaro tsakanin Chadi da Nijar
Tagwayen zabukan Chadi sun gudana ne a wani yanayi na sauyi a fannin diflomasiyya, inda Faransa take ci gaba da janye sojojinta daga kasar bayan rugujewar yarjejjeniyar tsaro da aka kulla bayan da Chadi da samu 'yancin kai.