Kalubale a Zaben 'yan majalisun dokoki a Benin
January 6, 2023Talla
A zaben da aka gudanar a shekara ta 2019 an samu karanci jama'a da suka fito,da riginginmu da suka kai ga fatatakar 'yan adawar da soke intanet. A yau, yawancin fitattun 'yan adawar na Benin ko dai suna yin gudun hijira ko kuma suna kulle a gidajen Kurkuku. Hamshakin attajiri Patrice Talon wanda aka zabeshi a shekarar ta 2016, aka sake kuma zabensa a shekarar ta 2021 ya kaddamar da sauye-sauye na siyasa da tattalin arziki da nufin dora kasarsa kan turbar ci gaba. Sai dai 'yan adawa na cewar a zuwansa kan karagar mulkin an samu gaggarumin koma baya na dimukradiyya, a kasar da ta yi zaman madubi na dimukaradiyyar a nahiyar Afirka.