'Yan al-Shabaab sun kai hare-hare a Kenya
June 14, 2015Wannan fada ya faru ne sakamakon kutsawa da 'yan bindiga na al-Shabaab suka yi sansanin Baure na sojojin Kenya tare da mamaye garin Lamu da ke da iyaka da kasar ta Kenya da kuma Somaliya.
kafafen yada labarai sun ruwaito cewa daga cikin wadanda suka rigamu gidan gaskiya har da 'yan bindiga 11. Sannan kuma rundunar sojojin Kenya ta yi ikirarin kwato makamai da damai daga hannu mayakan al-Shabaab.
Wannan ya zo ne shekara guda bayan jerin hare-hare da 'yan al-Shabaab suka kai garin Mpeketoni da kewaye inda suka kashe mutane fiye da 100 da nufin tilastawa gwamnatin ta Kenya janye sojojinta daga Somaliya. Sannan kuma a watan Afirilu ma dai tsagerun na Somaliya sun kai hari jami'ar Garisa inda suka kashe mutane 148 galibinsu dalibai.