'Yan al-Shabaab sun sake kwace wasu wurare
July 3, 2015Talla
A cewar hukumomin kasar, janyewar dakarun na Tarayyar Afirka ya shafi yankuna Qoryoley da Awdhegele wadanda suka sake fadawa a hannayen 'yan kungiyar ta al-Shabaab.
A cewar mazauna wannan yanki, tuni dai 'yan kungiyar ta al-Shabbab suka kafa tutarsu a garuruwan da suka kwace, kuma babu sojan kiyaye zaman lafiya ko daya a yankin da ke a nisan km akalla 80 da Mogadiscio babban birnin kasar.
Daga nashi bangare Shugaban gundumar ta Awdegele Mohamed Aweys ya tabbatar cewa shi ma ya fice daga wannan birni.