'Yan bindiga sun bude wa wani otel wuta a Cote d'Ivoire
March 13, 2016Talla
Wadanda suka gane wa idanuwansu sun shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewar 'yan bindigar wadanda suke sanye da kallaye a fuskokinsu, sun bude wa katafaren otel din shakatawar da ke shake da mutane a cikinsa wuta.
Kawowa yanzu dai hukumomin birnin Abidjan na kasar ba su bayyana ko mutane nawa ne suka mutu da kuma kasashen da suka fito ba.
Hare-hare a kan manyan otel-otel dai na cigaba da zama ruwan dare a kasashen Mali da Burkina Faso, a inda a 'yan kwanankin baya sai da wasu 'yan bindigar suka budewa wasu a kasashen wuta tare da hallaka da dama da ke yawan shakatawa da gidajen otel din.
Tuni hukumomin tsaron Cote d'Ivoire suka dukufa domin gano wadanda suka kai harin.