'Yan bindiga sun kai hari a Burkina Faso
October 9, 2015A Burkina Faso jami'an tsaro uku sun halaka a a cikin wani hari da wasu mutane kimanin 50 dauke da makamai suka kaddamar a wannan Juma'a a barikin jami'an tsaro na Jendarma ta garin Samorogouan da ke a Yammacin kasar kusa da kan iyaka da kasar Mali.
Ofishin ministan tsaro na kasar ta Burkina Faso wanda ya tabbatar wa da kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP da abkuwar wannan lamari ya ce da misalin karfe hudu na daren jiya ne mutanen dauke da makammai da kawo yanzu ba a tantance ko suwa ne ba suka kawo harin a garin na Samorogouan da ke a nisan kilomita 400 a Arewa maso yammacin birnin Ouagadougou.
Babban hafsan sojin kasar ta Burkina Faso Janar Pingrenoma Zagre wanda ya tabbatar da kashe daya daga cikin maharan, ya yi kira ga al'umma da ta kontar da hankalinta domin sun dauki karin matakkan tsaro dan kare lafiyarsu.