1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira na ƙasar Somaliya na cikin wani mawuyacin hali

July 19, 2011

A na ci-gaba da samun yawan mutuwa na 'yan gudun hijira na ƙasar Somaliya wɗanda ke a cikin sansanoni na yan gudun hijira na ƙasar Habasha

https://p.dw.com/p/11zrD
Mata da yara na ƙasar Somaliya na karɓar abinciHoto: dapd

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato HCR ,ta ce kaso na addadin waɗanda ke mutuwa na yan gudun hijira na ƙasar Somaliya a ƙasar Habasha.Ya ƙaru galibi yara ƙanana saboda rashin abinci mai gina jiki . wani jami'in hukumar Paul Spiegel ya ce lamarin ya ƙazance a sansani yan gudun hijira na garin Dolo Ado:

Inda yara yan ƙasa da shekaru biyar ke mutuwa ba ƙaƙautawa;mutane kimanin miliyion goma sha biyu ne a yankin na kusurwar Afirka ke fama da matsalar yuwan;a sakamakon farin da ake fama da shi wanda ya shafi ƙasashen Djibouti da Kenya da Habasha da kuma Yuganda .

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Eidita : Ahmad Tijani Lawal