'Yan gudun hijira na ƙasar Somaliya na cikin wani mawuyacin hali
July 19, 2011Talla
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato HCR ,ta ce kaso na addadin waɗanda ke mutuwa na yan gudun hijira na ƙasar Somaliya a ƙasar Habasha.Ya ƙaru galibi yara ƙanana saboda rashin abinci mai gina jiki . wani jami'in hukumar Paul Spiegel ya ce lamarin ya ƙazance a sansani yan gudun hijira na garin Dolo Ado:
Inda yara yan ƙasa da shekaru biyar ke mutuwa ba ƙaƙautawa;mutane kimanin miliyion goma sha biyu ne a yankin na kusurwar Afirka ke fama da matsalar yuwan;a sakamakon farin da ake fama da shi wanda ya shafi ƙasashen Djibouti da Kenya da Habasha da kuma Yuganda .
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Eidita : Ahmad Tijani Lawal