'Yan sandan Jamus na binciken 'yar ta'addar nan Daniela
February 29, 2024'Yan sandan Jamus sun sanar da kawo karshen binciken da suke gudanarwa a gidan da tsohuwar 'yar ta'addar nan Daniela Klette ta kungiyar Red Army Faction ta zauna a birnin Berlin, inda suka samu tarin makamai a Alhamis din nan.
Karin bayani:'Yan sandan Jamus sun cafke wani mutum da ya yi garkuwa da 'yarsa mai shekara 4
A ranar Litinin din da ta gabata ne 'yan sandan suka kama matar mai shekaru 65, bayan ta yi badda bamin sauya suna, kamar yadda suka wallafa a shafinsu na X, sannan suka kwashe mazauna ginin baki-daya don gudanar da bincike.
Karin bayani:'Yan sandan Jamus sun gano sakon kai hari a kasar
'Yan sandan dai na zargin Klette da aikata miyagun laifukan fashi da makami da yunkurin kisan kai a lokuta da dama daga shekarar 1999 zuwa 2016, karkashin kungiyarta ta Red Army Faction wato RAF, wadda aka kafa a shekarar 1968 don aikata muggan laifuka.