1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan jihadi sun halaka mutane a kasar Burkina Faso

Abdoulaye Mamane Amadou
May 20, 2019

Mayakan jihadi a Burkina Faso sun kaddamar da wani harin ta'addanci tare da halaka mutane bakwai ciki har da fararen hula hudu a wani kauyen da ke kan iyakar kasar Burkina Faso da Mali.

https://p.dw.com/p/3ImrQ
Mali Geiselnahme Hotel in Bamako
Hoto: imago/PanoramiC

Wasu mutane da ake kyautata zaton mayakan jihadi ne sun hallaka mutane bakwai ciki har da jami'an tsaro uku da wasu fararen hula hudu a garin Kouri da ke kan iyakar Kasar Mali da Burkina Faso.

Masu aiko da rahotanni sun ruwaito wani jami'in tsaro da bai so a ambaci sunanshi ba na cewar daga cikin fararen hular hudu da hatsarin ya rutsa da su, har da wasu direbobin motocin dakon kaya biyu 'yan kasar Ghana da ke tsaye kan iyakar kasashen na Mali da Burkina Faso mai cike da hada-hada. 

Shedun gani da ido sun tabbatar wa manema labarai da cewar maharan sun isa a garin ne kan babura da mota, kafin kuma ka ce kwabo suka fara buda wuta a yain da daga bisani kuma suka gudu.