'Yan ta'adda sun kai harin bam a Somaliya
May 8, 2017Talla
Rahotanni na cewa akalla mutane shida ne suka muta yayin da wasu goma kuma suka ji jiki a wani harin bam da aka kai a Mogadishu babban birnin kasar.
Rundunar jami'an 'yan sandan kasar ta ce harin ya faru ne lokacin da wata mota dauke da nakiyoyi ta tarwatse a wani wajen da ke kusa da ofishin hukumar shige da ficen kasar. Tuni kuwa kungiyar Al Shabaab ta dauki alhakin harin na ranar Litinin, kungiya ta tarzomar cikin gida mai alaka da Al Qaeda.
Mayakan na Al Shabaab dai sun yi kaurin suna da kaddamar da munanan hare-hare a birnin na Mogadishu da ma ratsin wasu garuruwa na kasar.