Al-Shabaab ta kashe gwamna a Somaliya
March 30, 2020Wasu 'yan sanda da malaman asibiti a yankin ne suka tabbatar da haka ga kamfanin dillancin labarai na AFP a wannan Litinin bayan harin da aka kai wa ayarin motocinsa a yankin Puntland na kasar.
Rahotanni sun ce bayan harin kunar bakin waken da aka kaddamar, gwamnan ya samu munanan raunuka, daga nan kuma aka ruga da shi zuwa asibiti. Sai dai kuma bayan kamar awa daya likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu.
Tuni ma dai kungiyar ta'addanci ta Al-Shabaab ta fitar da sanarwar cewa ita ce ta kaddamar da wannan mummunan harin.
Tun a shekara ta 2011 dai dakarun gwamnati suka yi nasarar kwace iko da birnin Mogadishu daga hannun 'yan Al-Shabaab kuma tun daga nan kadarinsu ya fara karyewa amma kuma 'yan ta'addar sun kwace wasu kauyuka da har yanzu sune ke da iko da su. Burin Al-Shabaab dai shi ne ta hambarar da gwamnatin kasar Somaliya wacce Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita, dalilin ke nan da ya sa take ci gaba da kaddamar da irin wadannan hare-haren a duk lokacin da ta sami dama.