Burkina Faso:'Yan bindiga sun kashe mutum 160
June 6, 2021Talla
Yanzu haka dai an yi jana'izar mutanen, wadanda suka hada da mata da yara da maza wadanda aka yi wa bisar jam'i a cikin manyan ramuka guda uku. Babu dai wata kungiya kawo yanzu da ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin, sai dai ana kyautata zaton cewar masu jihadi ne suka kai harin. Wannan shi ne hari mafi muni da 'yan ta'addar suka kai a Burkina Faso tun bayan harin da ya afku a shekara ta 2015 wanda a ciki mutane 30 suka mutu galibi 'yan kasahen waje.