1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

241214 Terror in Afrika: Al-Schabaab

December 31, 2014

Kisan gilla a yankin arewacin Afrika, da fafutukar masu tsananin kishin addini a Mali, gami da 'yan al-Shabaab sun gallabi kasashen Afirka

https://p.dw.com/p/1EDZT
Hoto: Imago/Xinhua

Kisan gilla a yankin arewacin Afrika, da fafutukar masu tsananin kishin addini a Mali, zuwa hare-haren kungiyar Boko haram a Najeriya, sun kasance batutuwa na ta'addanci da suka fi daukar hankalin kafafen yada labaran duniya a shekara ta 2014. Kungiyar Al-shabaab da ta ta yi fice a Somaliya da gabashin Afrika.

Kungiyar ta Al-Shabaab dai ta dauki tsawon shekatru tana fafutukar kafa shari'ar musulunci a fadin kasar, kuma ya zuwa yanzu tana da alaka ta kut da kut da sauran kungiyoyi masu tsananin kishin addini dake wasu kasashen Afrika.

Al Shabaab Sympathisanten Festnahme 08.12.2014 Mogadischu
Hoto: Reuters/F. Omar

Ga Ali Hassan da ke aiki a wani shagon aski na zamani dai, wannan sabuwar rayuwa ce. 'Yan watanni ke nan da ya fara aiki a wannan dan karamin wurin aski a babban birnin kasar wato Mogadishu. Tsawon wannan lokaci ya kulla kyakkyawar dangantaka da Kwastomominsa.

A baya dai ya kasance fitaccen dan kungiyar ta Al-Shabaab, amma tuni ya fice inda ya hade da hukumar tsaron kasar ta Somaliya. Duk da cewar wannan dama ce da ya samu na sake rayuwa kamar sauran mutane, rayuwar ta kasance cikin tsoro saboda barazanar da yake fuskanta daga 'yan shohuwar kungiyarsa ta Al-Shabaab.

A kusan kowane mako dai Ali yana samun kiran waya na yi masa barazana. Tuni dai aka kashe wani da suka fice daga kungiyar tare. Amma duk da haka a shirye yake a kullum wajen bayyana yadda rayuwarsa ta kasance a kungiyar ta Al-Shabaab.

al-Shabaab Kämpfer in Somalia
Hoto: picture alliance / AP Photo

Ali Hassan dai ya bayyana yadda ya tsinci kansa a wannan kungiya a matsayin dalibi mai nazarin ilimin addini, daga bisani kuma suka samu horo a fannoni daban-daban a kan mayaka na fafutuka. Daga nan kuma ya san masaniyar yadda alakar kungiyoyin dama sirrin yadda suke tafiyar da harkokinsu na kasa da kasa da kafa Ressa. Alal misali Larabci don matasa na Al Shaabab, wani reshe ne na al Qaeda da ke da wakilai tsakanin 7,000 zuwa 10,000. Wannan reshe shike da alhakin sace mutane marasa adadi da hare-hare kan 'yan siyasa, da ma'aikatan agaji da 'yan jarida. Baya ga Somaliya, kungiyar tana kai hare-hare a kasashen da ke makwabtzaka na Uganda da Kenya.