'Yan wasan da suka fi jefa kwallo a wasan zakarun Turai
Ganin irin kwallon da suka zura a wasanni uku na neman cin kofin zakarun nahiyar Turai, dan wasa Robert Lewandowski na kungiyar Barcelona da Thomas Müller na Bayern Munich sun kasance mafiya zura kwallo a tarihin gasar.
Zlatan Ibrahimovic - kwalaye 48
Dan wasan gaba na Sweden, babu mamaki Zlatan Ibrahimovic ya jefa kwallaye 48 a gasar zakarun Turai a kungiyoyi guda shida: Ajax Amsterdam (6), Juventus (3), Inter Milan (6), FC Barcelona (4), AC Milan (9 ) da Paris St Germain (20). Bai taba samun nasarar lashe gasar zakarun Turai ba, (har zuwa watan Oktoba 2022).
Andriy Shevchenko - kwallaye 48
Kamar Ibrahimovic, shi ma dan kasar Ukraine yana da kwallaye 48 a gasar zakarun Turai, amma ba kamar dan Sweden ba, shi ya yi ritaya tun tuni. A shekara ta 2003, Shevchenko ya samu nasara da kungiyar AC Milan ta Italiya. Dan wasan ya jefa kwallaye 29 lokacin da yake AC Milan, sannan 15 da Dynamo Kyiv kana hudu da kungiyar Chelsea.
Alfredo di Stefano - kwallaye 49
Dan wasan gaba na Ajentina ya yi wasa da Real Madrid na shekaru 11. A lokacin ana kiran wasan zakarun nahiyar Turai da sunan Kofin Turai. Sau biyar a jere daga 1956 zuwa 1960 yana samu nasarar lashe gasar, godiya ga kwallaye 49 da Alfredo di Stefano ya jefa. Dan Ajentina yana cikin 'yan wasan da suka yi fice a duniya lokacin. Alfredo di Stefano ya mutu a shekara ta 2014.
Thierry Henry - kwallaye 50
Dan wasan gaba na Faransa ya taimaka aka zura daruruwan kwallaye a gasar zakarun Turai a tsawon wasannin da ya yi: AS Monaco (7), Arsenal FC (35) da FC Barcelona (8). Lokacin da yake Barcelo a shekarar 1998 ya lashe gasar. Akwai mutum-mutumin Thierry Henry a filin wasan Arsenal.
Thomas Müller - kwallaye 53
Gasar zakarun Turai da Thomas Müller sun kulla da juna. Lokacin da yake shekaru 19 da haihuwa ya fara zura kwallo na farko daga cikin kwallayensa. Daga inda ya nuna bajinta sun hada da lokacin da Bayern Munich ta doke Sporting Lisbon 7 da 1 a watan Maris na 2009. Sau biyu yana lashe gasar a 2013 da 2020 (har zuwa watan Oktoba na 2022).
Ruud van Nistelrooy - kwallaye 56
Dan wasan tsakiya na Netherlands, Rutgerus Johannes Martinus van Nistelrooij sunansa na asali ke nan, ya jefa kwallaye yayin da ya yi wasa a kungiyoyi uku a gasar zakarun Turai: PSV Eindhoven (8 ), Manchester United (35) da Real Madrid (13). Duk da haka bai samu nasarar lashe gasar ba, amma sau uku yana zama wanda ya fi jefa kwallaye a raga.
Raul Gonzalez Blanco - kwallaye 71
Raul ya zama abin nuni a kungiyar Real Madrid. Ya shafe tsawon lokacin a matsayin jagoran 'yan wasa fiye da kowanne dan wasa. Ya yi wasanni 550 a lig na Spain kana 132 a gasar zakarun Turai kadai. Sau uku yana samun nasara da kungiyar Real Madrid. Raul ya jefa kwallaye biyar daga cikin 71 a gasar zakarun Turai lokacin da ya yi shekaru biyu a kungiyar FC Schalke 04.
Karim Benzema - kwallaye 86
Lokacin yana shekaru 18 da haihuwa ya fara jefa kwallo a gasar zakarun Turai, lokacin yana tare da kungiyar Olympique Lyon. Tun shekara ta 2009, Benzema yana cikin tawagar Madrid da suka samu nasara a gasar zakarun Turai. Dan wasan na Faransa tun shekara ta 2019 yana wasa daure da kyalle a hannu sakamakon raunin da ya samu, ko samu abin da ya yi imani ko kuma saboda shawarar likitoci.
Robert Lewandowski - kwallaye 91
A matsayi na uku tsohon dan wasan Bayern Munich, Lewandowski wanda ya lashe gasar zakarun Turai kuma sau biyu dan wasan da ya fi shahara a duniya. Dan kasar Poland ya samu duk nasarra a shekara ta 2020. Ya jefa kwallaye 17 yana Borussia Dortmund, 69 yana Bayern Munich kana sau biyar yana FC Barcelona (har zuwa Oktoba na 2022).
Lionel Messi - kwallaye 127
Idan kungiyar FC Barcelona tana batu daga 2004 zuwa 2021, Lionel Messi yana kan gaba. Dan kasar Ajentina sau 120 yana jefa kwallaye tare da Barcelona a gasar zakarun Turai, yanzu yana Paris St. Germain.
Cristiano Ronaldo - kwallae 140
Gagarumin dan wasa daga kasar Portugal ya lashe gasar zakarun Turai sau biyar. Duk inda ya yi wasa Manchester United (21), Real Madrid (105) ko Juventus Turin (14), Cristiano Ronaldo yana da tabbas a kusan kowanne wasa. Sau biyar yana zama gwarzon dan wasa kuma na gaba a fitattun 'yan wasa a wasannin Turai.