Yau Litinin an kaddamar da sabuwar majalisar dokokin Somaliya
August 20, 2012A karon farko cikin shekaru 20, yau Litinin ake ƙaddamar da sabuwar majalisar dokokin ƙasar Somaliya, a Mogadishu babban birnin ƙasar.
MDD ta ce sabbin 'yan majalisun za su samu kariya daga dakarun kiyaye zaman lafiya na ƙungiyar Tarayyar Afrika, inda ake gudanar da bikin a filin saukan jiragen sama na Mogadishu, da ke samun kariyar dakarun na kiyaye zaman lafiya.
Bayan zaɓen sabon kakakin majalisa, 'yan majalisu suna da aikin zaɓen sabon shugaban ƙasa, kuma ana saran Shugaba Sheikh Sharif Sheikh Ahmed, da ke kan madafun iko tun shekara ta 2009, zai iya lashe zaɓen, amma akwai wasu 'yan takara.
Akwai kimanin dakarun Tarayyar Afirka 17,000 da ke aikin tabbatar da zaman lafiya. Yau wa'adin gwamnatin da ke samun tallafin MDD ya kawo ƙarshe, kuma tunda fari, an zaci samun sabon Shugaban ƙasa, amma yanzu an bayyana tsaiko kan zaɓen sabon shugaban.
Mawallafi: Suleiman babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi