1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan 'yan gudun hijira ya ragu a Jamus a 2017

Abdullahi Tanko Bala MNA
January 17, 2018

Alkaluman kididdiga da ma'aikatar cikin gida ta Jamus ta fitar ya nuna an sami raguwar yawan yan gudun hijira da suka nemi mafaka a Jamus a bara.

https://p.dw.com/p/2qzge
Bundesamt für Migration und Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Stratenschulte

Alkaluman kididdigar da ministan cikin gida na Jamus Thomas de Maiziere ya baiyana a ranar Talata a birnin Berlin sun nuna cewa a yanzu tururuwar da 'yan gudun hijira ke yi domin shigowa Jamus ya ragu matuka, inda ya ce an sami raguwar mutane fiye da dubu dari daya idan aka kwatanta da shekarar 2016.

"Yawan wadanda suka nemi mafaka a karon farko a nan Jamus ya sake raguwa matuka a shekarar 2017 idan aka kwatanta da shekarar 2016. A 2017 yawan mutanen ya kai mutum dubu 186. Yayin da a waccan shekarar 2016 adadin ya kai mutum dubu 280."

Ministan cikin gidan ya kara da cewa 'yan gudun hijira musamman daga Gabas Ta Tsakiya da kuma Afghanistan sun ci gaba da zama kalubale na gama gari ga nahiyar Turai baki daya. Sai dai ya ce suna hada karfi da karfe domin shawo kan matsalar.

'Yan Siriya su ne mafi yawa da adadin 'yan gudun hijira fiye da dubu 47 yayin da 'yan Iraki suke da kimanin dubu 21 sai kuma 'yan Afghanistan su fiye da dubu 12, inji ministan na cikin gida Thomas de Maiziere.

Deutschland Bundespressekonferenz zur Entwicklung und aktuellen Zahlen der Flüchtlinge
Shugabar ofishin kula da 'yan gudun hijira Jutta Cordt da ministan cikin gida Thomas de MaiziereHoto: picture-alliance/AP Photo/M. Sohn

"A hakika kimanin kashi 40 cikin 100 ko kuma a ce kashi 43 cif cikin 100 na masu neman mafaka sun sami amsa mai armashi kuma za su iya ci gaba da zama a Jamus. A saboda haka wannan na nufin cewa za su iya zama a nan tsawon lokaci. Shi yasa shirin sajewar baki yake da matukar muhimmanci a garemu. Shi ne muhimmin abin da muka sa a gaba."

Farin ciki ga jam'iyyun da ke mulki

Wannan dai labari ne mai dadi ga jam'iyyun siyasa da ke cikin gwamnati. An takaita yawan masu neman mafakar siyasar zuwa kasa da adadin da aka iyakance na dubu 200 kamar yadda masu ra'ayin rikau da dama suka yi turjiya a kai.

Ko ba komai wannan zai rage lugude da matsin lamba da sha sukar da gwamnatin ke fuskanta a kan batun na 'yan gudun hijira a daidai lokacin da ake kokarin kafa gwamnatin hadin gwiwa da jam'iyyar SPD.

Yawan 'yan gudun hijirar da suka shigo Jamus a bara sakamakon rikicin Siriya da Iraki da kuma Afghanistan bai kai na 2016 ba.

De Maiziere ya ce wannan ya samu ne sakamakon rufe kan iyakokin kasashen yankin Balkan da kuma mashigin tekun Bahar Maliya, wadanda a baya 'yan gudun hijira ke amfani da su wajen shiga kasashen Turai.

Ya kara da cewa hukumar kula da 'yan gudun hijira ta yi aiki tukuru wajen toge mutanen da suka nemi mafaka a shekarun baya. Yana mai cewa hukumomin Jamus sun iya tantance hakikanin bayanan 'yan gudun hijirar ta amfani da na'urorin binciken kimiyya da wayoyinsu na salula da kuma harshen da suke magana da shi.