1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yoshihiko Noda: firaministan Japan na gaba?

August 29, 2011

Ministan kuɗin Japan Yoshihiko Noda ne zakaran da Allah ya nufa da cara, a zaɓen fit da ɗan takara da zai yi zawarcin kujerar firaminista ƙarƙashin tutar jam'iyar Democratic Party da ke mulki.

https://p.dw.com/p/12PCU
Yoshihiko Noda, ɗan takaran firaministan Japan na DPHoto: AP

Jam'iyar Democratic Party da ke kan karagar mulkin Japan ta zaɓi ministan kuɗin ƙasar Yoshihiko Noda a matsayin ɗan takara da zai yi mata zawarcin kujerar firaminista, bayan da Naoto kan ya bayyana aniyarsa na wanke hannayensa daga harkokin mulki sakamakon daƙushewar farin jini da ya ke fiskanta. Ɗan takaran Yoshihiko Noda na da tabbacin zama firaminista na gaba, saboda ita Democratic Party na da gagarumin rinjaye a majalisar dokokin da ke zaɓan firaminista.

Firaministan kan mai barin gado wanda ya shafe watanni 15 ya na jagorancin ƙasar da ke zama ta biyu a ƙarfin tattalin arziki a duniya, ya na shan suka ne game da rashin taɓukan wanin abin a zo a gani lokacin da Japan ta fiskanci tagwayen bala'o'i da suka haɗa da girgizar ƙasa, da lalacewar tashar makamashin nukiliya da kuma igiyar ruwan Tsunami.

'Yan takara biyar ne dai suka fafata tsakaninsu a zagayen farko da nufin zaman gwanin wannan jam'iya, kafin gudanar da zagaye na biyu tsakanin Noda da kuma ministan tattalin arziki Banri Kaiedo. kamar dai sauran 'yan takara da suka sha kaye, Noda yayi alƙawarin mayar da tattalin arzikin Japan kan kyakyawar turba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal