1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin gina cibiyar tunawa da Sankara

Mouhamadou Awal Balarabe
October 3, 2017

Shekaru 30 bayan kisan gillar da aka yi wa jagoran juyin juya hali na Burkina Faso Thomas Sankara, gidauniyar da aka sanya wa sunansa na fadi-tashi don tattara kudi da nufin gina mutum-mutuminsa a matsayin girmamawa.

https://p.dw.com/p/2l9WO
Thomas Sankara ARCHIV
Hoto: Getty Images/AFP/A. Joe

Thomas sankara wanda aka haifa a ranar 21 Disemban 1949 ya yi mulkin soja a Burkina Faso daga 4 ga watan Agustan 1983 zuwa 15 ga Oktoban 1987. A tsukin lokacin da ya shafe a kan kujerar shugabanci, ya canja sunan kasarsa daga Haute Volta zuwa Burkina Faso, saboda adawa da ya nuna ga angizon da faransa da ta yi kasar mulkin mallaka ke da shi a kasar. Ya tashi tsaye wajen yaki da cin hanci da rashawa, tare da samar da hanyoyin da 'yan kasa za su amfana da arzikin da Allah ya hore musu.

Wannan dalili ne ya sa membobin gidauniyar raya manufofin Sankara suke ganin cewar ya dace a samar da wani abin tunawa da shi  Dan fafutuka Smockey ya ce "Thomas Sankara jan gwarzo ne, saboda haka ya dace a samar da wani guri ko cibiya da matasan Afirka za su iya haduwa, don tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban Afirka. Ta irin wannan hanya ce za a iya raya manufofin da Sankara ya fara assasawa, domin ciyar da kasashenmu gaba."

Burkina Faso Erinnerung an Präsident Thomas Sankara
'Yan Burkina Faso na ci gaba da girmama SankaraHoto: Getty Images/I. Sanogo

 Shi dai Thomas sankara ya rungumin wani salon mulki da kowane dan kasa na da irin gudunmawar da yake badawa, imma kudi ne ko taimakawa da shawarwari. Ko da wadanda ke kokarin koyi da shi na bin wannan hanya wajen samar da kudin gina cibiyar tunawa da shi.

Da yawa daga cikin magoya bayan Sankara na Burkina Faso na sanyashi a sahun su Kwame Nkrumah na Ghana a fannin wadanda suka nuna matikar kishin Afirka.

Noufou Zougmmore, mai nazarin harkokin siyasa ya ce "Kun san cewar a Ghana akwai mutum-mutumin Kwame Nkrumah da aka gina. Kun ga cewar akwai bukatar yin koyi da wannan mataki. Wannan zai nuna cewar a kwana a tashi Sankara ya yi gaskiya."

Sai dai mai dakin Thomas Sankara wato Mariam Sankara ta bukaci a ci gaba da bincike don gano wanda ya yi maigidanta kisan gilla.