Samar wa karnuka abinci a Najeriya
May 22, 2019A kwai dai karnuka sama da miliyan goma a Najeriya mutane na amfani da su a gidaje da gonaki don biyan bukatunsu a inda wannan adadin ke matikar bukatar samun wata masarrafar abinci hakan ya sa matasan biyu a Abuja suka ga rashin abinci na musamman don dabbobin wata babbar matsala ce ba wai ga iyayen gidan dabbobin ba har ma da dabbobin su kansu.
Wadanan dai na daya daga cikin irin tarin dalilan da Lubem Ugbu da Chibuze matasa masu kyakkyawan fata a nan gaba suka hada kai domin fara sarrafa abincin karnuka kamar dai yadda suka bayyana.
Matashi Lubem Ugbor: "Na fara lalubar abubuwan da suka dace domin na ciyar da karnukana kuma na yi ta kokarin yadda zan sayi abinci a gidajen sayarwa sai dai samun ragowar abincin da mutane suke ci su rage a guraren sayar da abinci to amma karena baya so, wannane ne ya sanya na zabura domin lalubo wa kaina mafuta tare da fara assasa yadda zan samar da abincin."
To amma ga Chibuze OKechikwu kuwa: "Ni kuwa karena mutuwa ya yi sabili da cin wani abinci da ban san inda ya je ya ci ba kuma abincin mai guba ne, wannan ne ya sanya na fara tunanin yadda zan fara ciyar da karena domin mutuwar sa na ji ba dadi."
Mafi yawancin abincin dai da mutane suka rage na da yaji a cikinsu a don haka ya rage wa karnunkan ko dai su ci ko kuma su hakura to amma Lubem da Chibuze sai suka yunkura domin fara samar da bincin wanda ke tattare da sinadarai da suka kunshi vitamins domin gina jikin karnukan.
Inanna Namani wani matashi ne wanda yake sayan abincin domin karensa: "A karon farko yanzu na ga karena yana cin abincin saboda yana so kuma wannan yana da nasaba da irin yadda ake sarrafa abincin wanda ya dace karnuka su ci."
Matasan dai na shafe rabin awa kafin harhada abincin sannan su sake kwashe rabin awa su dafa kuma komi a tsare yake tare da aunawa a yayin da tuni kasuwarsu ta bude a tsakanin masu karnuka a Abuja da kewaye.