An gaza cimma matsaya tsakanin Eu da Birtaniya
December 7, 2020Bayan shafe daren jiya ana tattaunawa tsakanin wakillan kungiyar tarayar Turai da na Birtaniya kan makomar kasuwancin bangarorin biyu gabanin ficewar Birtaniyar daga kungiyar ta EU, an gaza cimma matsaya a tattaunawar. Machel Barnier na kungiyar EU da takwaransa daga bangaren Birtaniya David Frost sune suka tattauna a Birnin Brussels na kasar Beljiyam kan yarjejeniyar kasuwanci tsakanin bangarori guda biyu, wadda za a cigaba da ita nan gaba.
Yarjejeniyar kasuwancin dai za ta maida hankali ne kan haraji da kuma shige da ficen kaya tsakanin Birtaniyar da kasashe mambobin kungiyar Tarayar Turai.
Nan gaba kadan ne a ranar Litinin din nan shugaba Boris Johnson na Birtaniya da shugabar kungiyar ta EU Ursula von der Leyen za su tattauna ta wayar tarho kan batun, gabanin babban taron EU a ranar Alhamis.