1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cibiyar rigakafin Corona ta farko zata fara aiki a Jamus

November 24, 2020

Jamus da kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince dasu fara amfani da maganin cutar Corona a kasashensu, inda Jamus zata bude cibiyar a tsakiyar watan Disamba mai kamawa.

https://p.dw.com/p/3ljwa
Deutschland Bundestag Änderung des Infektionsschutzgesetzes Jens Spahn
Hoto: Sean Gallup/Getty Images

Biyo bayan samun maganin cutar COVID-19 da aka yi, gwamnatin Jamus zata bude cibiyar rigakafin cutar Corona ta farko a kasar. 

Ministan lafiya na kasar Jens Spahn shine ya tabbatar da hakan a wata tattaunawar da aka yi da shi. Ministan ya ce tuni ya bukaci gwamnatocin jihohin kasar dasu ware cibiyoyin da za a fara wannan aikin, kamin nan da tsakiyar watan Disamba mai kamawa.

Tuni dai kasar ta Jamus ta tanadi alluran rugakafin sama da miliyan 300, haka ma lamarin ya ke a mafi yawancin kasashen kungiyar Tarayyar Turai wadanda suka amince da ingancin maganin.

Adadin wadanda suka kamu da cutar ta Corona a Jamus din yanzu haka ya kai 942,687 inda 14,361 suka rigamu gidan gaskiya sanadiyar cutar.