Sahel: Taron kan tsaro
February 12, 2021Talla
A kokarinta na kawo karshen hare-haren da masu ikirarin jihadi ke kaiwa a yankin Sahel, gwamnatin Chadi za ta kara yawan dakarunta a iyakokin kasashen Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso da Mali.
Kimanin dakarun sojin dubu ne ake sa ran rarrabawa a iyakokin, bayan da Chadin ta yi tunanin agazawa dakarun Faransa da na Tarayar turai da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin.
Kasar ta Chadi ta ce za ta yi bayanin dalla-dalla yadda rabon zai kasance a wajen taro kan matsalar tsaron yankin da za a gudanar a mako mai zuwa a Birnin N'jamena.
A shekarar da ta gabata dai Faransar ta yi ikirarin samun nasara kan mayakan jihadin da ke tada zaune tsaye a yankin.