1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa cikin fargabar tsaro a Somaliya

Yusuf Bala Nayaya
February 8, 2017

Mambobi na dukkanin 'yan majalisar kasar, majalisar dokoki 275 da majalisar dattawa 54 na jefa kuri'unsu a wani akwatin kada kuri'a da ake iya ganin abin da ke cikinsa.

https://p.dw.com/p/2XAhU
Somalia Präsidentschaftswahl
Hoto: Reuters/F. Omar

An fara kada kuri'a a zaben shugaban kasar Somaliya, zaben da ke wakana a yanayi na taka tsatsan saboda tsaro, lamarin da ya sanya aka rufe filin tashi da saukar jiragen saman babban birnin kasar da ma hana kara kaina ta ababan hawa a manyan titunan kasar.Mambobi na dukkanin 'yan majalisar kasar, majalisar dokoki 275 da majalisar dattawa 54 na jefa kuri'unsu a wani akwatin kada kuri'a da ake iya ganin abin da ke cikinsa, a wannan zagayen farko na zaben da 'yan takara 21 ke fafatawa.

Tsoron kai hare-hare daga Kungiyar al-Shabab ya sanya zaben ya takaita ga 'yan majalisa wadanda ke kada kuri'a a wani tsohon sansanin sojan saman kasar ta Somaliya a Mogadishu babban birnin kasar. Ana dai bada bayanai kan abin da ke faruwa a game da zaben ta kafar sadarwar intanet.