1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga - zanga a Burkina Faso

Pinado Abdu WabaFebruary 7, 2015

Jama'a sun fito nuna adawa ne da rundunar tsaron saboda cin zarafin da ta yi lokacin boren da ya hambarar da gwamnatin Compaore

https://p.dw.com/p/1EXnc
Burkina Faso Jubel nach dem Rücktritt des Präsidenten Compaore 31.10.2014
Hoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Dubban mutane ne suka fantsama kan tituna a Ouagadougu babban birnin ƙasar Burkina Faso domin buƙatar a rusa wata runduna ta musamman da ke bai wa shugaban ƙasa tsaro wadda ake tsoronta kwarai da gaske a ƙasar. Rundunar wadda aka fi sani da RSP na shan kakkausar suka saboda rawar da ta taka lokacin zanga-zangar da ya kai ga saukar tsohon shugaba Blaise Compaore daga mulkin da ya shafe shekaru 27 yana yi.

Aƙalla mutane 24 suka hallaka wasu 600 kuma suka yi rauni a wancan lokacin. Zanga-zangar ta ran Asabar wadda Ƙungiyoyin farar hula suka kira an yi shi ne a dandalin Revolution, dandalin da aka rika taruwa ana nuna adawa da Compaore.

Tun bayan saukar Compaore ƙasar na cigaba da kasancewa a hannun gwamnatin riƙo a ƙarkashin jagorancin Michael Kafando a matsayin shugaban ƙasa da Isaac Zida a matsayin Firaminista.