Zargin kasashe fursunoni a Burkina Faso
April 20, 2020Talla
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta zargin jami'an tsaron Burkina Faso da halaka fursunoni 31 wadanda aka kama ranar 9 ga wannan wata na Afrilu a garin Djibo lokacin samamen yaki da ta'addanci.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta ce ta yi magana da shaidun gani da ido 12 wadanda suka shaida abin da ya faru. Ana kyautata zaton mutanen da abin ya shafa kabilu ne na wasu makiyaya. Kungiyar ta Human Rights Watch ta nemi gwamnatin Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka ta yi binciken bisa lamarin da ke zama laifin yaki.
Mutane da dama sun halaka sakamakon hare-haren tsagerun masu kaifin kishin addinin Islama a kasar ta Burkina Faso tun daga shekara ta 2017.