1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Human Rights Watch ta zargi sojan Burkina

Abdoulaye Mamane Amadou
July 8, 2020

Kungiyar kare hakin bil'Adama ta Human Rights Watch ta yi kakkausar suka game da kisan mutane 180 a yankin Djibo da ke arewacin Burkina Faso, inda ta nuna 'yar yatsa ga jami'an tsaron kasar.

https://p.dw.com/p/3ewNw
Afrika 2017 | Burkina Faso | Soldaten im Einsatz
Hoto: Imago Images/ZUMA Press/B. Slessman

A cikin wani rahotonta kungiyar ta wallafa kungiyar ta ce an samu wasu kaburburan jama'a wadanda aka kashe haka suddan ba tare da yi masu shara'a ba a yankin Djibo na arewacin Burkina Faso 180, bayan ta gudanar da bincike da jin ra'ayin  jama'a, inda ta ce mutanen yankunan da kansu tare da agajin soja suka binne mamatan hade a cikin kaburbura a watanin Maris da Aprilun da suka gabata.

Ba tun yau ba dai ake zargin jami'an tsaron Burkina Faso da aikata kisan jama'ar da basu san hawa ba su san sauka ba a yakin da suke da 'yan ta'adda kan iyakokin kasar masu makwaftaka da  Mali da Nijar.