Zaɓen gama gari a Burkina Faso
November 29, 2015Talla
Kimanin mutane miliyan biyar ake sa ran za su fito a zaɓen wanda a da aka so yin shi a cikin watan jiya amma daga bisani aka ɗage saboda juyin mulkin da sojoji suka yi
Yan takara guda 14 za su fafata a zaɓen,kuma ana sa ran biyu daga cikinsu Roch Marc Christain Kabore tsohon firaminista a gwamnatin Blaise Compaoré da wani ɗan kasuwar Zéphirin Diabré za su iya samu nasara. A cikin watan Oktoba na shekara bara ne wani boren al'umma ya share gwamnatin Blaise Compaore a kan yunƙurinsa na yin wani sabon wa'adi bayan yayi shekaru 27 a kan karagar mulki