Zida ya zamo Firaministan Burkina Faso
November 19, 2014Talla
Zida dai shine ya karbi mulki a hannun tsohon shugaban kaar Blaise Compaore, da zanga-zangar nuna adawa da tazarce da 'yan Burkina Faso suka yi, ta tilasta masa yin murabus. Wani babban jami'in gwamnatin kasar ne ya sanar da hakan a yayin da yake karanta wata doka daga shugaban kasar na rikon kwayar Michel Kafando, wanda shima masu ruwa da tsakin suka amince da ya jagoranci kasar nan da shekara guda da za a mika mulki hannun farar hula a kasar.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Awal Balarabe