Ziyarar Niebel a Somaliya
March 31, 2012Ministan raya kasar Jamus Dirk Niebel ya kai wata ziyarar bazata a babban birnin Somaliya wato Mogadishu, domin goyon bayan yunkurin da ake yi wajen maido daidaito a kasar, wacce ta shafe shekaru 20 yanzu bata da gwamnati mai cikakken iko a tsakiya. A wata sanarwa da ta wallafa, Hukumar ta Dirk Niebel ta ce ministan ya isa Mogadishu a cikin wani yanayi na tsaro, kuma zai gana da da wakilan gwamnatin rikon kwaryar kasar, da na kungiyar Tarayyar Afurka da kuma kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya. Wannan ne karon farko da wani babban jami'in Jamus ke kai ziyara kasar, tun bayan da ta shiga wani yanayi na rudani daga farkon shekarun 1990. A wani taron kolin da ya gudana a watan Fabrairun da ya gabata, shugabanin duniya sun yi alkawarin bada gudunmawa wajen dakatar da ayyukan ta'addanci da na fashin jirgin ruwa a kasar amma bisa sharadin cewa mahukuntan kasar zasu zabura su girka gwamnati mai karfi a tsakiya.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Usman Shehu Usman