1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

270711 Somalia Hilfsorganisationen

July 27, 2011

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta fara jigilar cimaka ta jiragen sama zuwa Mogadishu, babban birnin ƙasar Somalia domin raba wa al'umar ƙasar da ke fama da ja'ibar yunwa.

https://p.dw.com/p/125CB
Masu fama da yunwa a SomaliyaHoto: dapd

Dafe dafe dai ba kama hannun yaro a ɗaya daga cikin sansanonin da aka tsugunar da ɗaruruwan 'yan Somaliya da su ka yi hijira daga yankunan da fari ya addaba zuwa Mogadishu. Da yawa daga cikinsu dai ƙawanya su ke yi wa maka-makan tukune da ke makare da abinci tun ma kafin a  sauke su daga wuta saboda sun shafe kwana da kwanaki ba tare da  sun sa wani abu a bakin salati ba.

Duk da cewa a halin yanzu ma tsarin na majalisar Ɗuniya ya tanadi tan goma sha huɗu na abinci da zai raba wa masu fama da yunwa a Somaliyan amma kuma rabashi na zama babban ƙalubale saboda haramcin ƙungiyar Al-shabab da ke ci gaba da aiki. Ko da su ma 'yan ƙasar da ke aikin na rabon abinci ciki kuwa har da Sharifa Abubakar Umar sayar da ran su su ke yi domin ceto rayukan bayin Allah da wannan bala'i ya shafa.

Hunger in Somalia Afrika
ƘoKon neman abinci na 'yan SomaliyaHoto: picture-alliance/dpa

Sharifa ta ce "A wasu lokuta tilas ka sakaye jikinka kafin ka yi wannan aikin. Da yawa daga cikin 'yan Al-Shabbab ba su iya karatu da rubuta ba. Ba sa iya rarrabe wanda ke aiki ƙarƙashin wata ƙungiya da sauran, saboda haka akwai babban haɗari a tattare da wannan aiki"

Galibin 'yan Somaliya da ke aikin na raba abinci da kuma ayyukan jin ƙai gujewa na alaƙa da kafofin watsa labarai domin gujewa kisa daga ɓangaren masu kishin addini. Hasali ma dai 'yan Al-shabbab din sun bindige wasu ma'aikata biyu har lahari sakamakon zarginsu da aka yi da haɗa kai da abin da su ka kira haramtattaun ƙungiyoyi sai dai kuma cin karensu da 'yan Al-shababa din ke yi ba babbaka a akasarin ƙasar da Somaliya bai sa sun juya wa 'yan uwansu baya kwata kwata ba.

Shugaban kungiyar DBG da ke zaman kanta wato Omar Olad ya ce ba za su taɓa gajiya ba matiƙar za su ci gaba da samun tallafi daga tarayyar jamus kamar yadda su ka saba.

Omar ya ce ''Yan al-Shabbab sun san mu, sun san cewa ba mu dau ɓangare ba. Na san  da dama daga cikinsu. Sun san kuma ba mu da wata alaƙa da harkokin siyasa"

Sai dai kuma har yanzu ƙungiyar al-Shabab da ke da kashi uku bisa huɗu na kasar ta Somaliya, na ci gaba da iƙirarin cewa babu fari da kuma yunwa a ƙasar. saboda haka za su sa ƙafar wando guda da duk wata kungiya da ta shigo ƙasar da sunan raba abinci ga waɗanda wannan bala'in ya shafa.

Cikin wannan mawuyacin hali ne, wata kungiya ta ƙasar Ireland da ta shafe shekaru 25 ta na gudanar da aiki jin kai, ta ke ci gaba da samarwa da wannan rashen na ta da karin kudin da ya bukata.

Somalia Hungersnot Schlange von Menschen vor Ausgabe von Lebensmitteln in Mogadishu
Jerin gwanon masu neman abinci a SomaliyaHoto: dapd

Shugaban rashen gabashin Afirka na kungiyar Organisation Concern ya ce hakarsu ta cimma rauwa ne saboda amfani da karin maganan da su ke yi wato 'da ɗan gari a kan ci gari'.

Shugaban ya ƙara da cewa ''ma'aikatanmu 'yan Somaliyan ne amma a ƙasar Sin aka haifesu kuma su ka girma. Sun san duk bukatun 'yan uwansu, sun fi kuma imaninsu, da kuma sanin yadda ya kamata su gudanar da aiki."

Da yawa daga cikin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da ke gudanar da ayyukan jin kai ne su ke haɗa kai da 'yan asalin ƙasar domin cimma muradun da su ka sa a gaba duk da haɗarin da ke tattare da wannan yunƙuri na su. Daga cikin waannan ƙungiyoyi kuwa har da Red Cross ko Red Cresent, da Medecins Sans Frontiers da makamatansu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Edita: Ahmed tijjani Lawal