1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙaruawar fargaba a Japan

March 26, 2011

Tsiyayar da dagwalon sinadarin nukiliya ke yi a Japan, masana suka ce zai ɗau lokaci kafin dakatar da shi

https://p.dw.com/p/10hoL
Injiniyoyi a tashar nukiliya ta fukushima.Hoto: AP

Hukumar kula da makashin nukiliya ta duniya wato IAEA tace bata sun iya lokacin da za'a dauka kafin injiniyoyi a ƙasar Japan su samu damar liƙe sinadarin nukiliya da ke yoyo a tashar makashin nuliyar Fukushima ba. Jami'ai a helkwatar hukumar IAEA dake birnin Viyana sun shaidawa manema labarai cewa, baya ga shaidar da ake da ita na yoyon da tukunya ta ɗaya da ta biyu ke ke yi, a yanzu suna zargin cewa ita ma tunkuyar sarrafa makashin nulkilya ta uku ta na fuje kuma dagwalon sinadarin nukiliya na fita daga gareta. Babban jami'in kula da kariya a hukumar yace za'a ɗauki lokaci kafin injniyoyi su iya ƙyasta yawan ɓarnar da aka samu. Firai ministan ƙasar Japan Naoto Kan yace, shawo kan matsalar tashar nukiliya ta Fukushima yana da sauran lokaci. Yanzu dai hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane kimanin dubu goma, yayin da wasu dubu 17 suka ɓace, biyo girgizar ƙasa da tsunami wada ya aukawa ƙasar.

Zanga zangar gyamar nukiliya a Jamus

Atom Japan Parteien Regierung
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: dapd

A halin da ake ciki kuwa, a ƙasar Jamus dubban masu adawa da shirin nukiliyar ƙasar ne suka yi zanga-zanga a sassa daban-daban na ƙasar a yau. Masu zanga-zangar dai sun ƙara harzuƙane bayan abinda ke fauwa a ƙasar Japan ya ƙara ƙamari. Zanga-zangar ana gudanar da ita ne a biranen huɗu mafi girma a ƙasar ta Jamus, waɗanda suka haɗa da Berlin, Hamburg, Munich da Kolon. Masu zanga zanagr dai suna neman tursasawa gwamnatin ƙasar ta rufe ɗaukacin tashoshin makamashin nukiliyar ƙasar. Wannan dai wani koma baya ne ga gwamnati mai ci, dumin a gobe ne ake gudanar da zaɓe a jihohin Bade-Wüttemberg da Rheineland-Pilatinate, kuma idan dai jam'iyya mai mulki ta faɗi a jihohin, to hakan wata han'yace ta fitar da ita daga fadar gwamnati a zaɓe mai zuwa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Mohammed Abubakar