1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen duniya sun yi alƙwarin tallafa wa Somaliya

February 23, 2012

Babban taron duniya a London ya sha alwashin sa ƙafar wando guda ga masu kawo ciƙas ga zaman lafiya a Somaliya.

https://p.dw.com/p/149Dw
British Prime Minister David Cameron, bottom row third right, gathers for a group photograph with delegates during the London Conference on Somalia at Lancaster House in London, Thursday, Feb. 23, 2012. Nations must help Somalia's fragile leadership tackle terrorism, piracy and hunger or be prepared to pay the price, Britain's leader warned Thursday at an international conference on the troubled east African nation's future. About 50 nations and international organizations attended a one-day summit hosted by Prime Minister David Cameron in London, including Somalia's Western-backed transitional government, U.S. Secretary of State Hillary Rodham Clinton and United Nations Secretary-General Ban Ki-moon. (Foto:Matt Dunham-Pool/AP/dapd)
Hoto: AP

Wani babban taron ƙasa da ƙasa kan makomar Somaliya da aka gudanar a wannan Alhamis a birnin London, yayi alƙawarin ɗaukar matakai kan abin da ya kira masu yi wa shirin samar da zaman lafiya ƙafar ungulu. A cikin sanarwar bayan taro, jami'ai daga ƙasashe 50 da ƙungiyoyi sun ce har yanzu ana cikin halin rashin sanin tabbas a Somaliya, kuma ana buƙatar taimakon gaggawa daga gamaiyar ƙasa da ƙasa. Mahalarta taron sun yi alƙawarin ruɓanya ƙoƙarinsu na maido da zaman lafiya da lumana a ƙasar da yaƙi ya ɗaiɗaita. Tun da farko an jiyo firaministan Birtaniya mai masaukin baƙi David Cameron na cewa 'yan Somaliya da kansu ne za su iya warware matsalolinsu.

"Ba mu taru a nan ne domin gabatar da wata maslaha daga nesa ga wata ƙasa ba, mun haɗu a nan ne domin faɗa wa al'umar Somaliya abin da ya kamata su yi. Muna bayanku, muna goya wa ƙoƙarin da kuke na sake gina ƙasarku baya."

Ita ma sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton da ta halarci taron na birnin London ta ce gwamnati a Washington za ta matsa ƙaimi don ganin sanya takunkumin hana tafiye tafiye da ɗora hannun kan kuɗaɗen ajiya waɗanda ke kawo ciƙas ga samun ci-gaban siyasa a Somaliya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadisou Madobi