Ƙoƙarin shawo kan matsalar fari a Somaliya
August 8, 2011Amurka ta ce za ta agazawa ƙasar Somalia da tsabar kuɗi dala miliyan 105 domin tunkarar bala'ain yunwar da ya yi mata katutu.
Wannan dai na fitowa ne a daidai lokacin da matar mataimakin shugaban ƙasar ta Amurka Jill Biden za ta ziyarci ƙasar tare da wasu jiga-jigan gwamnatin ta Amurka domin ganewa idonsu halin da ake ciki, inda za su ziyarci sansanonin da aka tsugunar da waɗanda yunwa ɗaiɗaita.
Yayin wannan rangadin dai, Mrs Biden za ta ziyarci sansanin Dadaab sannan za ta gana da ministar aiyyukan gona ta Ƙasar Kenya Sally Kosgie domin tattauna batutuwa da dama da su ka shafi halin da ake ciki a Somaliyan.
A watan da ya gabata ne dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewar wasu ɓangarori biyu a kudancin ƙasar na fama da bala'in yunwar da ba a taɓa ganin irin ta ba cikin shekaru 60 ɗin da su ka gaba.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Saleh Umar Saleh