Ƙungiyar AU za ta tura sojoji dubu shida Somaliya
July 27, 2010Shugabannin ƙasashen Afirka da ke taro a ƙarƙashin lemar ƙungiyar AU a birnin Kampala na Yuganda, sun amince da ƙara yawan dakarunsu a ƙasar Somaliya. Ministan harkokin wajen Ethiopiya Seyoum Mesfin ya shedawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, taron ya amince da tura ƙarin sojoji dubu shida domin tabbatar da zaman lafiya a Somaliya dake fama da hare-haren ƙungiyoyi irin su al -Shebab.
Yanzu haka dai akwai sojoji 600 da ga ƙasashen Yuganda da Burundi. A ranar 11 ga wannan watan ne dai ƙungiyar al-Shebab ta ɗauki alhakin wani harin ta'addanci da ya hallaka mutane 76 a birnin Kampala, a wani mataki da ƙungiyar ta kira shiga sharo ba shanu da Yuganda keyi a harkokin cikin gidan Somaliya.
A yau ake fatan kammala taron ƙungiyar na AU da ake gudanarwa a duk shekara wanda kuma ake fatan zai ɗauki matakan inganta tsaro da lafiya da kuma bunƙasar tattalin arziki da zamantakewar nahiyar baki ɗaya.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Yahouza Sadissou Madobi