1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta taimaka wa Afirka da dabarun tsaro

April 17, 2018

 A ci gaba da neman mafitar rikicin rashin tsaron da ke bazuwa zuwa kasashen Afirka, manyan hafsoshin kasashen da na Amirka sun gana a Abuja da nufin neman mafita ga matsalar da ke zama karfen kafa.

https://p.dw.com/p/2wCVy
Westafrikas Staatschefs bei ECOWAS Summit
Zauren taron nazarin tsaron nahiyar AfirkaHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Kama daga ita kanta mai masaukin baki Najeriya ya zuwa daukacin kasashen yankin Sahel da ma tsakiya da wani sashe na gabashin nahiyar Afirka irin Kwango dai babu alamun kakkautawar  rikici a daukaci na nahiyar ta Afirka. Nahiyar da ke da dumbin albarkatun kasa dai na kuma fuskantar tarin rigingimu ko na akida ko kuma gwagwarmaya ta nema na bakin salati  ko kuma neman mulki a kasashen. Abin kuma da ya dauki hankalin manyan hafsoshin tsaro na kasashen nahiyar da suka taru a Abuja sannan kuma ke neman kawance da manyan kasashen duniya irin su Amirka da nufin tunkarar matsalar.

Nigeria Vize-Präsident Yemi Osinbajo
Hoto: Novo Isioro

Hanyoyin nasara a tunanin Janar Gabriel Olanishakin da ke babban hafsan tsaro Najeriyar dai shi ne hada karfi da nufin toshe hanyoyin samar da kudi na tayar da hankalin. Ta’addanci, da safarar jama’a da yaduwar kananan makamai game da fashi na barayin jiragen ruwa na ci gaba da zama barazana ga Afirka.

A yayin da duniya ke fuskantar sababbin nau’o’in rashin tsaro da ke da tayar da hankali, hafsoshin tsaro a kasashen na Afirka da kawayensu na bukatar hada kai da nufin tunkarar annobar mai tasiri. Saboda haka akwai bukatar hada kai mai karfi a tsakanin kowa da nufin toshe kafafen kudade ga duk wasu kungiyoyin da ke iya zama barazana ga kasashe ko kuma yankuna da ma nahiyar mu gaba daya. Wannan hadin kan zai tabbatar ne in muka kulla  ingantacce na kawance da hadin kan da zai  kare muradi da bukatu  da nufin tabbatar da tsaro a nahiyar Afirka.

Afrika Senegal US Soldaten
Wasu dakarun Amirka a AfirkaHoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Duk da cewar dai akwai alamun bambancin muradu a tsakanin kasashen, akwai sha’awa a bangaren kawayen na kasashen na Afirka da ke fadin akwai alamun hada karfi tare. Janar James Mc Connel babban hafsa ne a hedikwatar sojojin kasar Amirka da kuma ya ce Amirkan na shirye wajen atisaye da kasashen na Afirka domin ba da taimako da karin karfi ga kasashen.

“Sojojin kasar Amirka na farin cikin shiga duk wani kawance da ma atisaye da kasashen na Afirka da dama. Kuma sojan Amirka a shirye suke da aiki da kasashen Afirka wajen tunkarar kalubalen rashin tsaro dake fuskantarmu a yau.

Ana dai sa ran wani atisaye na hadin gwiwa a tsakanin sojan tarrayar Najeriyar da na Amirka a wani barikin sojoji da ke wajen birnin Abuja.