SiyasaAfirka
An sace 'yar Austria a Jamhuriyar Nijar
January 13, 2025Talla
Ma'aikatar harkokin wajen Austria ta sanar da sace wata mata 'yar kasar a birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar.
A cikin wata sanarwa da ta aike wa kamfanin dillancin labarai na AFP, ma'aikatar ta ce dole ne a tabbatar da aukuwar lamarin.
An sako Turawan da aka sace a yankin Sahel
Da farko sanarwar ta ce an shaida wa ofishin jakadancin Asutria da ke birnin Algiers na Aljeriya da Nijar ke karkashinsa batun garkuwa da matar.
Wata kafar yada labarai a Agadez mai suna Air Info ta ce sunan matar da aka sacen Eva Gretzmacher 'yar shekara 73, kuma ta shafe shekaru 28 ta na zaune a birnin na Agadez.
Faransa na zargin garkuwa da jakadanta
Hukumomin kasar ta Austria sun ce suna aiki tare da abokan hulda don sanin halin da matar ke ciki da kuma kubuto da ita.