Ana cece-kuce bayan dage gasar cin kofin Afirka na CHAN
January 15, 2025Hukumar kwallon kafa ta kasashen Afirka ta dage gasar CHAN da ake shirin gudanarwa a Kenya da Tanzaniya da Yuganda zuwa watan Agusta bisa rashin ingancin wurareen wasanni da gidajen sauke baki. Wannan matakin na zuwa ne, sa'o'i kalilan kafin CAF ta samar da jadawalin gasar ta 'yan kwallon Afirka da ke bugawa a cikin gida.
Karin bayani :Labarin wasanni: na ranar 13.01.2025
A ka'idance, cikin makonni biyu masu zuwa ne hukumar ta ayyana cewa za a soma buga gasar. Tuni ma dai mai horar da 'yan wasan Angola ya bayyana bacin ransa kan wannan mataki, yana mai cewa duk da kokarin da hukumar CAF ke yi na inganta wasannin kwallon kafa, bai dace a ce an dage gasar mai matukar muhimmanci kwanaki 15 kacal a gabanin fara ta ba.
Karin bayani : Labarin wasanni: Kammala wasan sojojin Afirka
Daga 1 zuwa 28 ga watan Fabreru ne ya kamata a gudanar da gasar CHAN a kasashen Kenya da Tanzaniya da Yuganda, wadanda su ne za su shirya gasar AFCON a 2027.