Myanmar: Sojoji sun kwace madafun iko
February 1, 2021Tuni aka baza jami'an tsaro a manyan titunan kasar tare da katse hanyoyin sadarwa da kuma kamar Internet, bayan da jam'iyyar da ke mulki ta hambararriyar Shugaba Aung San Suu Kyi ta yi tir da juyin mulkin da sojojin suka yi. Sojojin dai sun bayar da sanarwar juyin mulkin a wani gidan talabijin mallakin rundunar sojojin kasar, tare kuma da kame Shugaba Aung San Suu Kyi gami da wasu jiga-jigan jam'iyyarta ta NLD, bayan zargin magudin zaben da ya gudana a watan Nuwambar bara.
Karin Bayani: Aung San Suu Kyi ta yi jawabi a kan batun Rohingya
A cikin sanarwar da sojojin suka bayar, sun bayyana sanya dokar ta baci a kasar tare da ci gaba da kula da harkokin mulki nan da shekara guda. Sai dai an zargi masu juyin mulkin da yin wannan kutsen ne, sakamakon gaza samun rinjaye ga jam'iyyar da suke marawa baya a zabubbukan na bara, inji Farfesa Melissa Crouch malama a wata jami'a da ke kudancin Wales a Birtaniya. Tun a wancen lokacin ne sojojin suka matsa kaimi, tare da bai wa 'yan siyasa wa'adi domin sake duba sakamakon zaben a kuma maida wa jam'iyyun da aka yi wa magudin kujerunsu, wanda hakan ya ci tura.
Janar Min Aung Hlaing wanda shi ne shugaban rundunar sojojin kasar, zai ci gaba da jagoranci tare da shirya wani sabon zaben domin mayar da mulki ga hannun farar hula nan da shekara guda mai zuwa. Sai dai masu rajin kare hakkin dimukuradiyya, na ganin cewa an riga an yi mata kafar baya. Phil Robertson mataimakin darakta a kungiyar Human Right Watch da ke kula da yankin Asiya, na cikin masu wannan tunani: ''Abin da ya fito fili karara shi ne sojoji sun yi wa dimukuradiyya karantsaye domin kawai jam'iyar NLD ta samu rinjaye, wanda ya sa dare daya suka mayar da kasar ta Bama halin da take sama da shekaru 10 da suka gabata. Maganar gaskiya wannan ba karamin koma baya ba ne.''
Karin Bayani:Bukatar kawo karshen kisan 'yan Rohingya
Duk da katse hanyoyin sadarwar da sojojin suka yi shugabar gwamnatin da aka hambarar da jam'iyyarta sun mai da martani, inda Aung San Suu Kyi ta bukaci sojojin da su koma barikinsu yayin da ita kuma jam'iyya mai mulkin ta bukaci 'yan kasar da su yi watsi da yunkurin rundunar sojojin kasar. Tuni suma kasashen duniya da suka hada da makwabtan kasar ta Miyanmar ko Bama kamar su Indiya da Thailand da kuma Japan, suka fara sukar wadanda suka yi juyin mulki da ka iya janyo wa kasar ta fuskanta takunkumi daga kungiyoyi da kasashen duniya.