Nijar: Chaina za ta ci gaba da ayyukanta
September 7, 2023Jim kadan bayan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar ta Nijar ne Chainan ta sanar da dakatar da ayikin gina babban dam din na Kandadji da zai bai wa kasar damar samun isasshen hasken wutar lantarki ba tare da dogaro da wasu kasashe ba, saboda rashin kudin gudanar da aikin. Sai dai kuma wadannan kalamai da suka fito daga jakadan Chainan a Jamhuriyar ta Nijar Jiang Feng da ya ce kasarsa na bai wa kasashen Afirka kwarin gwiwa kan sasanta duk wani rikici nasu a tsakaninsu ba tare da wani ya yi musu katsalandan ba, na nuna aininhin matsayarta kan rikicin.
Karin Bayani: Man fetir alheri ko akasin haka a Nijar
A cewarsa a kan haka ne gwamnatin Chaina ta yi tayin shiga tsakani kan matsalar da ake fuskanta a Jamhuriya ta Nijar, tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yuli. A fuskar ci gaba da hulda tsakanin kasashen biyu na, jakadan Chainan a ya ce aikin da suke yi tsakanin 'yan Nijar da 'yan Chaina, don haka suna yi ne domin ci-gaban al'umomin kasashen biyu.
Da yake tsokakci kan wannan batu, wani dan kungiyar farar hula masu fafutukar nuna kishin kasa da kare mutuncin kasa Ibrahim Namaiwa ya ce huldar Chaina da Nijar ba ta yanzu ba ce. Wannan batu dai, na samun goyon baya daga al'ummar Jamhuriyar Nijar din mazauna kasashen waje. Guda daga cikin 'yan Nijar mazauna Faransa kuma shugaban wata kungiya ta kare hakkin dan Adam da ci-gaban dimukuradiyya ta SEDEL/ DH Nijar Abdoulaye Idrissa Boureima da mai lakanin Alhaji Baba Almakiyya ya ce, ya kyautu kasarsa ta biyu ta Faransa ta fahimci cewa lokaci ya sake.
Karin Bayani: Bankado badakalar cin hanci a harkar mai a Nijar
Kasar Chaina dai ta kasance babbar abokiyar hulda a fannin kasuwanci da Jamhuriyar Nijar musamman a fannin makamashi, inda kasashen biyu ke shimfida wani mafi tsawo a Afirka. Bututun da ke da nisan kilo mita 2000 zai tashi ne tun daga mahakar mai ta Agadem zuwa tashar ruwan Seme da ke kasar Benin, wanda kamfanin CNPC na kasar ta Chaina da ya gina matatar mai ta SORAZ da ke Damagaram ke gudanar da shi.